logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta yi karin haske kan fashewar bututun Nord Stream

2023-02-15 16:13:26 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Fashewar bututun iskar gas na Nord Stream da ya auku a watan Satumban bara, ya sake jawo hankalin duniya a kwanakin baya, sakamakon yadda shahararren dan jaridan Amurka, Seymour Hersh ya ruwaito cewa, gwamnatin Biden ce ta tsara shirin lalata bututun wanda kasar Rasha ke amfani da shi don jigilar iskar gas dinta zuwa kasashen Turai.

Duk da cewa kwamitin tsaron kasa na fadar White House, da hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka wato CIA, da ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ma sauran sassan gwamnatin Amurka duk sun musanta rahoton, amma bisa yin la’akari da sunan Seymour Hersh a fagen watsa labarai na Amurka, da ma cikakkun bayanai da aka rubuta filla filla game da lamarin, ana ganin cewa, ruwa ba ya tsami a banza.

Ko mene ne gaskiyar lamarin? Ya zama dole a kara yin bincike don tabbatar da amsa. Amma wani abin da muke iya tabbatarwa shi ne Amurka ce ta fi amfana da lamarin fashewar bututun, kasancewar bututun ya dade yana damun kasar Amurka, musamman ma bayan aukuwar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine, ’yan siyasar Amurka sun san cewa, muddin dai bututun yana nan, ba zai yiwu kasashen Turai da Rasha su bata kwata kwata ba. Kaza lika abun da ya faru, ya tabbatar da cewa, kawo yanzu ba kawai Amurka ta cimma moriyar siyasa daga rikicin Rasha da Ukraine ba ne, har ma ta samu muguwar riba daga isar gas da ta sayar wa kasashen Turai a kan farashi mai tsada.

Idan ba a manta ba, a makwanni kafin aukuwar rikicin, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi gargadin cewa, idan dai Rasha ta kaddamar da yaki a kan kasar Ukraine, “za mu kawo karshen Nord Stream-2”, bayan da bututun ya fashe kuma, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, “ya zama babbar nasara a karshe”, wanda zai taimaka wa Turai wajen “daina dogaro ga Rasha ta fannin makamashi”. To, sai yanzu ne muka gane abin da suke nufi.

Bututun iskar gas na Nord Stream, muhimmin aikin more rayuwa ne da aka gina tsakanin kasa da kasa. Kuma lalacewarsu ya haifar da mummunar illa ga kasuwar makamashi, gami da muhallin halittun duniya, don haka dole a hukunta wadanda suka aikata laifin lalata shi.

Idan an tabbatar da gaskiyar rahoton binciken da dan jaridan Amurka Hersh ya wallafa, to, lamarin ya zama aikin ta’addanci da wata kasa ta aikata ke nan, wanda sam ba za a iya amincewa da shi ba. Haka kuma, ya zama dole Amurka ta maida martani game da shakkun da kasa da kasa ke nunawa a kan ta, da bada hadin-kai don binciken musababbin aukuwar lamarin, saboda duniya na bukatar adalci da sanin gaskiya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)