logo

HAUSA

Kasar Sin ta ciri tuta a fannin bunkasa noma da raya karkara domin neman ci gaba mai inganci

2023-02-15 15:26:56 CMG Hausa

A farkon makon nan ne gwamnatin kasar Sin, ta fitar da kundin koli na farko a shekarar nan ta 2023, mai kunshe da manufofin raya noma da bunkasa yankunan karkara, wanda a cikinsa, babbar manufar raya karkara ta kasar Sin, ta kasance raya yankuna daga bangarorin masana’antu, da al’adu, da muhalli, da samar da kwararrun ma’aikata, da dai sauransu. Kana makasudin manufar ita ce neman zamanintar da aikin gona da kauyukan kasar Sin, ta yadda za a kai ga cimma nasarar samar da isasshen abinci a kasa baki daya, da tabbatar da cewa mutanen da suka fita daga kangin talauci ba su sake komawa ba, da kuma gina kauyuka masu kayatarwa da ban sha’awa.

Muna iya cewa, wannan kundi na kunshe ne da ci gaban manufofi da kasar ta Sin ta jima tana aiwatarwa, a fannin raya karkara, da kara kyautata fannin noma, duba da muhimmancin hakan ga rayuwar daukacin al’aummar kasar. Kamar dai yadda Bahaushe kan ce “Da ruwan ciki ake jan na rijiya”, wato dai babu wata harka ta ci gaban bil adama da za ta yi nasara, idan har ba a iya samar da isasshen abinci ba.

Kuma sakamakon wadannan manufofi da gwamnatin Sin ke aiwatarwa, sannu a hankali, adadin hatsin da kasar ke girbewa a duk shekara yana karuwa, inda a shekarar 2022 da ta gabata, adadin ya kai kilo biliyan 686.5, wato ya karu da kilo biliyan 3.7 kan na shekarar 2021. 

Kaza lika a shekarar bana ma, mahukuntan kasar Sin suna kara taka rawar gani, wajen aiwatar da matakai daban daban na raya aikin gona, da bunkasa kauyuka, da rayuwar manoma, lamarin da ya taimakawa ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar kasar. 

Wadannan nasarori, kari ne kan sakamakon da aka samu a fannin yaki da talauci, matakin da ya sa kudin shigar manoman kasar yake ta karuwa sannu a hankali. A daya hannu, mazauna karkarar Sin, sun ci gajiyar fardado da sassan kiwon lafiya, da fannin ciyar da sana’o’in su gaba. (Saminu Hassan, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)