Hadarin jirgin kasa ya nuna yanayin hakkin dan Adam da Amurka ke ciki
2023-02-15 13:38:17 CMG Hausa
A ranar 3 ga wannan watan nan ne wani jirgin kasa ya kauce daga kan layin dogon da yake bi, ya kuma kama da wuta a garin East Palestine, dake jihar Ohio ta kasar Amurka.
Rahotannin wasu kafofin watsa labarai na kasar sun labarta cewa, taragu kusan 50, na jirgin kasan dakon kayayyakin sun kauce daga kan layin dogon, ciki har da taragu goma, wadanda ke dauke da sinadarai masu guba.
Ya zuwa ranar 6 ga wata, hukumar daidaita matsalolin gaggawa ta jihar, ta tsai da kudurin kone iska mai gubar da ta fita, bisa taimakon kwararru. Kuma gwamnatin jihar ta sanar da cewa, mazauna garin suna iya komawa gidajensu a ranar 9 ga wata, saboda hadarin bai gurbata muhalli ba.
To sai dai kuma wasu da suka koma garin sun kamu da nau’o’in rashin lafiya daban daban, don haka suka bayyana bukatar ganin gwamnatin kasar ta sanar da su tasirin gurbatar muhallin garin sakamakon wannan hadari, da matakan da za ta dauka domin dakile matsalolin.
Sai har zuwa yanzu, hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin Amurka, ba su sanar da adadin sinadarai masu guba da suka fita ba, kuma kafofin watsa labaran kasar su ma ba su gabatar da rahotanni kan batun yadda ya kamata ba, kana yayin da ministan sufurin kasar Pete Buttigieg yake halartar wani biki a ranar 13 ga wata, ya yaba da kayayyakin more rayuwar jama’ar da ake ginawa kadai, inda ya kauda kai daga batun hadarin jirgin kasan.
Ko shakka babu, ya dace jami’an gwamnatin Amurka su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin martaba hakkin dan Adam, tare kuma da kare tsaron rayukan al’ummar kasa, maimakon yadda ‘yan siyasar kasar, da rukunonin dake goyon bayansu, su gurgunta moriyar jama’a, domin kare moriyar kansu, lamarin da ya sa yawancin Amurkawa suke cikin mawuyacin yanayi. (Jamila)