Wakilin kasar Sin ya yi kira da a yi kokarin rage dumamar yanayi da dakile saurin tunbatsar teku
2023-02-15 13:44:36 CMG Hausa
Wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga al’ummar duniya, da ta gaggauta daukar dukkan matakan da suka wajaba, ta yadda za a iya dakile, da rage saurin karuwar dumamar yanayi da tunbatsar teku.
A jiya Talata ne dai kwamitin tsaron MDDr ya gudanar da taron muhawara, kan alakar tunbatsar teku da batun zaman lafiya, da tsaron kasa da kasa.
A jawabin da ya gabatar, Zhang Jun ya bayyana cewa, ya kamata al’ummar kasa da kasa ta karfafa nazari game da yadda za a rika yin hasashen tasirin tunbatsar teku. A sa’i daya kuma, a mai da hankali kan asalin dalilin dake haifar da matsalar sauyin yanayi, domin rage saurin dumamar yanayi, da kuma rage saurin tunbatsar teku.
Ya ce idan har ana son cimma makasudin kafa yarjejeniyar Paris, ya zama dole kasashe masu sukuni su shige gaban sauran kasashen duniya, wajen kara rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli.
Zhang Jun ya kara da cewa, kasashe masu sukuni, suna da nauyi da hakkin ba da tallafin kudi, da taimakon tinkarar sauyin yanayi ga kasashe masu tasowa. Kaza lika kasashe masu sukuni sun yi alkawari a shekarar 2009 cewa, za su rika ba da kudaden da suka kai dalar biliyan 100 ga kasashe masu tasowa a kowace shekara, amma har yanzu, ba a samu wadannan kudade ba tukuna.
Zhang Jun ya kara da cewa, mafita daya tilo da za a iya bi wajen tinkarar sauyin yanayi, ita ce nuna goyon baya ga tunanin cudanyar dukkanin sassa, da kuma karfafa hadin gwiwa. Kuma ya kamata a ci gaba da tsayawa tsayin daka kan “ka'idar sauke nauyi na gama-gari, amma bisa gwargwadon karfin kowane sashe”, wanda hakan ke da alaka da adalci tsakanin kasa da kasa. Ya ce idan aka gujewa wannan ka’ida, hakan zai gurgunta hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen duniya, a fannin tinkarar sauyin yanayi. (Safiyah Ma)