logo

HAUSA

Takunkumin Da Amurka Ke Sanyawa Kasar Sham Na Tsananta Matsalar Jin Kai Da Kasar Ke Fuskanta

2023-02-04 08:52:49 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, ran 6 ga wata, an yi girgizar kasa mai tsakani a kudancin kasar Turkiya dake dab da iyakar kasar Sham. Hukumar kiwon lafiya da dai sauran hukumomin ba da agaji na kasar sun ba da labari a ran 8 ga wata cewa, mutane a kalla 2500 sun mutu yayin da wasu 4000 suka jikkata.

“Muna matukar bukatar tallafi……”, bala’in ya rushe gidajensu, mutane da dama na karkashin buraguzai, ba a san ko suna da rai ko a’a ba, ana matukar bukatar tallafi daga waje. Amma, Amurka da dai sauran kasashen yamma na ci gaba da aiwatar da takunkumi kan kasar cikin dogon lokaci, matakin da ya sa kasar fuskantar karancin manyan na’urorin aikin ceto, ta yadda wadanda suka tsira da ransu a bala’in suna hako ‘yan uwansu ta amfani da hannu kawai. Abu ne mai matukar bakanta rai, ganin yadda jama’ar kasar suke yin kuka suna zubar da jini, har wasu ma sun mutu bayan da aka cetonsa saboda karancin jiyya!

Amma, Amurka ta yi kamar ba ta ji ba ta gani, to ko mene ne ma’anar ra’ayinta na kare hakkin Bil Adama, kuma don me ba ta bayar da tallafin jin kai a matsayinta na kasa mafi karfi a duniya? Dole ne ta yi watsi da yanke hukunci, wadannan mutane da bala’in ya ritsa da su ba su da isashen lokacin jira, bala’u ba za a iya guje musu ba, amma mu Bil Adama na iya zabar taimakon ‘yan uwanmu. (Mai zana da rubuta: MINA)