logo

HAUSA

Kungiyar Tarayyar Afirka za ta tura tawagar sanya ido kan babban zaben Nijeriya

2023-02-15 13:43:16 CMG Hausa

Hukumar zartaswa ta kungiyar Tarayyar Afirka AU ta sanar a jiya Talata cewa, za ta aike da wata tawaga mai kunshe da ma’aikata 90 zuwa Najeriya, domin ta sanya ido kan yadda babban zaben kasar na ran 25 ga watan Faburairu zai gudana. Kuma tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ne zai shugabanci tawagar.

AU ta bayyana cewa, makasudin tura tawagar shi ne tabbatar da ganin an gudanar da babban zabe bisa adalci kamar yadda ake fata, sannan za ta sanar da shawarwari game da yadda za a kara inganta zabukan kasar na gaba. 

Bugu da kari, kungiyar ta jaddada goyon bayata ga kokarin “karfafa dimokuradiyya, da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma neman ci gaba a Nijeriya”. (Safiyah Ma)