logo

HAUSA

Sin ta samar da tallafin kudin sayen abinci don taimakawa jama’a masu karamin karfi dake arewacin Togo

2023-02-15 14:33:02 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta ba da tallafin kudaden sayen abinci ga kasar Togo, ta hannun shirin samar da abinci na duniya WFP, don agazawa masu karamin karfi dake arewacin kasar.

Yayin bikin mika hatsin da ya gudana a jiya Talata, wakilin Sin dake Togo Chao Weidong, ya bayyana cewa, tallafin kudaden da Sin ta ware zai taimaka wa Togo sayen hatsi da yawansa zai kai fiye da tan 600, wanda zai amfani mutane wajen dubu 52, a yankunan Savannes da Kara.

Jami’in ya bayyana cewa, Sin tana fatan raba damarmakin ci gaba tare da sauran kasashen duniya, domin neman bunkasuwar dukkanin bil’adam tare.

A nasa tsokacin kuwa, wakilin shirin samar da abinci na duniya dake Togo Aboubacar Koisha, cewa ya yi, shirin tallafin abinci na gaggawa, ya taimakawa mutanen dake cikin tsananin bukata, da dawo da kyakkyawan fata, da kwanciyar hankali, da kuma karfin hadin gwiwar zamantakewa, na jama’ar yankin.

Koisha ya ce, “Kokarinmu zai canja rayuwar mutanen dake fama da tasirin kamfar abinci, da cimaka mai gina jiki”.

Tallafin na Sin, daya ne daga cikin tallafin abinci tan 961 da shirin abinci na duniya yake jagorantar rabawa, kuma manufarsa ita ce taimakawa jama’a masu karamin karfi dake arewacin Togo, wadanda suka hada da iyalan da sauyin yanayi ya shafa, da kuma mutanen da suka kauracewa gidajensu sakamakon matsalar tsaro. (Safiyah Ma)