Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin (3): Dawo da kayan tarihin Sin zuwa gida
2023-02-15 21:03:59 CMG Hausa
Kayan al’adun tarihi, da sauran abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni, suna dauke da kwayoyin halittar mu, da tsatson kasar Sin. Albarkatu ne da ba za a iya sabunta su ba, ko maye gurbin su da wasu na daban, suna kuma dauke da kyakkyawar wayewar kai ta al’ummar kasar Sin. Kwamitin kolin JKS, mai shugaba Xi Jinping a matsayin jigo, na dora muhimmanci sosai ga dawo da kayan tarihin Sin zuwa gida.
Tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, wanda ya gudana a shekarar 2012, Sin ke kara kaimi wajen dawo da irin wadannan kayayyaki mallakin ta zuwa gida. Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama, ta kuma shiga tsarin hadin gwiwa da kasashe 24 game da hakan. Inda matakin ya haifar da dawo da kayan tarihin kasar sama da 1,800 zuwa gida. (Saminu Alhassan)