logo

HAUSA

Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a Afrika ta shaida zumunci na kut da kut tsakanin sassan biyu

2023-01-17 08:52:00 CMG HAUSA

Abokai, yanzu haka sabon ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, yana ziyarar aiki a wasu kasashen Afrika, ziyarar da ta kasance ta farko da Qin Gang ya kai kasashen ketare, tun bayan kama aikin sa a matsayin ministan wajen kasar. Kaza lika bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara kasashen Afirka.

Tun lokacin da take fuskantar talauci da koma baya a farkon kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin, Sin da kasashen Afrika sun taimakawa juna, da goyawa juna baya ta fannonin da suka shafi manyan muradunsu, don samun bunkasuwa tare cikin hadin kai, zuwa lokacin da Sin ta samu bunkasuwar a zo a gani a duniya, ba ta manta da abokanta na Afrika ba ko kadan, tana kuma kokarin raba musu fasahohi, da samar da tallafi don cimma moriya tare.

Kullum Sin na mai da kasashen Afirka a matsayin manyan kawayenta, kuma ziyarar ministan harkokin wajen kasar a nahiyar a farkon ko wace shekara ta tabbatar da dangantakarsu, kuma ci gaban da suke samu a bangarori daban-daban a cikin dogon lokaci ya shaida zumuncinsu. (Mai zane da sharhi: MINA)