logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin| (1): Mene ne mafarin “Sin”

2023-02-15 20:45:30 CMG Hausa

Shin ko yaushe ne aka fara ambatar sunan "Sin" cikin shekaru 5,000 da suka gabata? Ko muna iya zakulo inda aka fara ambatar "Sin" cikin tarin tsofaffin rubuce-rubuce da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni?

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci wurin tarihi na Yin dake birnin Anyang, na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin.

Yayin ziyarar da ya kai wurin a watan Oktoban bara, wadda ita ce ziyarar farko a cikin gida, da ya gudanar bayan babban taron wakilan JKS na karo na 20, shugaban ya ambato muhimmancin binciken kayan tarihi da ake ganowa. Shugaba Xi ya ce za a ci gaba da zurfafa bincike, game da asalin wayewar kan kasar Sin.

Ya kara da cewa, “Fannin binciken kayan tarihi na amsa tambayoyi da dama, ciki har da fannonin ilimin falsafa, kamar batun “Ina ne asali na?” da “Ina na dosa?”, baya ga batun yin karin haske game da mafarin kasar Sin ita kan ta”. (Saminu Alhassan)