logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin (2): Na jima ina kewar Dunhuang

2023-02-15 21:01:12 CMG Hausa

Dunhuang, wurin da al’ummu 4 suka hadu da juna, wuri ne na Sin da kuma wasu karin sassan duniya. Dunhuang na kasan tsaunin Mingsha, kusa da kogin Dangquan, inda ginin jikin kogo na dakin bauta na Mogao Grottoes ke tsaye. Wannan makeken ginin kogo dake jikin magangarar tsauni, na bayyana labarin dubban shekaru da suka gabata. Shugaba Xi Jinping ya taba cewa "Ina kewar Dunhuang." Idan ka ziyarci Dunhuang, za ka kara amincewa da ra’ayin shugaba Xi, game da "Musaya da koyo daga juna tsakanin al’ummu mabambanta."  (Saminu Alhassan)