Za a wallafa rahoton Xi kan aikin tattalin arziki a mujallar Qiushi
2023-02-15 15:57:46 CMG Hausa
A gobe Alhamis ne za a wallafa muhimmin rahoto mai taken “Wasu muhimman batutuwa game da aikin raya tattalin arzikin kasar Sin a halin yanzu” da babban sakataren kwamitin kolin JKS, shugaban kasar kuma shugaban kwamitin aikin soja Xi Jinping ya gabatar a yayin taron da aka kira kan aikin raya tattalin arziki a yau Laraba, a mujallar Qiushi.
Rahoton ya bayyana cewa, akwai bukatar a mai da hankali kan muhimman fannonin tattalin arziki yayin da ake gudanar da aikin raya tattalin arzikin kasar a bana. A sa’i daya kuma, ya dace a kara habaka bukatun gida domin hanzartar gina tsarin sana’o’in zamani, tare kuma da kara samun jarin waje, ta yadda za a magance aukuwar rikicin hada-hadar kudi. Kana rahoton ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ingiza farfadowar kauyuka daga duk fannoni, da ci gaba mai inganci bisa shawarar ziri daya da hanya daya, tare da zurfafa kwaskwarima a kasar. (Jamila)