logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci NATO Ta Kauracewa Shafawa Sin Kashin Kaji

2023-02-14 20:30:39 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na kira ga babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, da ya kauracewa shafawa kasar Sin kashin kaji.

Wang ya yi tsokacin ne, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da zargin da Mr. Stoltenberg ya yi cewa, wai balan-balan din kasar Sin da ta shiga samaniyar kasar Amurka, na alamta karuwar ayyukan leken asiri da kasashen Sin da Rasha ke yi kan kasashe mambobin NATO.

Wang Wenbin, wanda ya mayar da martanin yayin taron manema labarai na yau Talata, ya ce kalaman jami’in na kungiyar NATO, zargi ne maras tushe, wanda aka kitsa shi musamman domin bata sunan kasar Sin. Don haka Sin ke kira ga NATO, da ta dakatar da furta kalaman bata sunan Sin, ta dakatar da kirkirar makiya na bogi, kana ta dakatar da kokarin fadada ikon ta, tare da rungumar manufofi masu ma’ana da za su wanzar da daidaito da zaman lafiyar kasa da kasa. (Saminu)