Magajin wasan Chao
2023-02-14 14:09:10 CMG Hausa
Zheng shunying ita ce magajin wasan Chao wanda ke da tarihi mai tsawon sama da shekaru 580, an samu asalin wasan ne a birnin Chaozhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Duk da cewa, tana da shekaru 60 da haihuwa yanzu, amma tana yin atisayen wasan ko wace rana, kuma tana koyarwa matasa wasan, saboda tana ganin cewa, muddin dai matasa suke kaunar wasa, sai dai wasan yana da makoma mai kyau. (Jamila)