Bangaren Sin ya nemi a janye dukkan takunkuman da wani bangare daya kadai ya kakkaba ba bisa ka’ida ba
2023-02-14 14:32:50 CMG Hausa

Zaunanen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nemi wasu kasashe masu alaka da ruwa, su gaggauta janye dukkan takunkuman da suka kakkaba wa wasu kasashe ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da shata wani sharadi ba, ta yadda za a iya baiwa yara damar rayuwa.
Mr. Zhang Jun ya yi wannan furuci ne, a yayin taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya Litinin, bisa jigon “Tasirin zubar da jini da rayuwar yara”.
Zhang Jun ya nuna cewa, bayan aukuwar bala’in girgizar kasa mai karfi ya auku a Sham, haramtaccen takunkumin da aka sanyawa kasar ya haddasa karancin manyan na’urori, da kayayyakin ceto a kasar, kuma sakamakon haka, yara masu dumbin yawa da gine-gine suka binne, sun rasa rayukansu, kasancewar ba za a iya gudanar da ayyukan ceton su a lokaci ba.
Zhang Jun ya kara da cewa, kamata ya yi a dauki matakan kandagarkin warware rikici, a matsayin mataki mafi muhimmanci, na kare wani ko wata kasa. Kuma bai kamata a dauki matakin amfani da karfin tuwo, kamar saka takunkumi ba gaira ba dalili ba, balle rura wutar rikici, ko ma a yi yunkurin tsanantawa, da kuma tsawaita wa’adin rikici, domin neman samun wata moriyar kashin kai.
Zhang Jun ya kara da cewa, ya kamata a aiwatar da ka’idar tafiyar da harkoki daban daban bisa doka, a matsayin babbar manufar kandagarki da ya kamata a bi.
Ya ce bangaren Sin yana kira ga sassan kasa da kasa, da kasar da har yanzu ba ta amince da “yarjejeniyar hakkin kare yara” ba, da ta hanzarta daukar matakan amincewa da ita, ta yadda wannan yarjejeniyar za ta iya fara aiki a duk fadin duniya a zahiri. (Safiyah Ma)
