logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sayo wasu kayayyakin aikin ’yan sanda daga China

2023-02-14 10:15:18 CMG Hausa

A ranar Litinin 13 ga wata, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da kayan aikin da rundunar ’yan sandan kasar ta sayo domin kara kyautata sha’anin tsaro a kasar.

Yayin bikin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar dake birnin Abuja, shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an ’yan sandan kasar da su kara himmatuwa wajen aikin tabbatar da tsaron kasa da kuma kare martabar demokradiyya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da cewa yana da kyau ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su kwana da sani cewa ’yan Najeriya da duniya baki daya sun zura musu ido domin ganin irin rawar da za su taka wajen ganin an gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali.

Ya ce, samar da wadannan kayayyakin ga rundunar ’yan sandan kasar alama ce dake nuna gamsuwa da irin kokari da kuma jajircewa shugaban ’yan sandan da sauran makarabansa wajen samun nasarar sabbin sauye-sauye da gwamnatinsa ta kawo a harkar aikin ’yan sanda a Najeriya.

Shugaba Muhamamdu Buhari ya ci gaba da bayanin cewa, bisa la’akari da matsayin da aikin ’yan sanda ya kai yanzu haka a Najeriya, akwai kyakkyawan sauye-sauye masu ma’ana sabanin yadda aikin yake kafin zamansa shugaban kasa yau kusan shekaru 8 ke nan, inda ya yi fatan cewa gwamnatin da za ta zo nan gaba za ta dora.

Shugaban na tarayyar Najeriya har ila yau ya ce kaddamar da kayan aikin da aka gudanar a ranar ta Litinin, yana daga cikin kudurce-kudurcen gwamnatinsa na wadata rundunar da kayan aiki irin na zamani domin tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a kasa da kuma samun nasarar zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.

“Na ji dadi sosai kan yadda shugabannin wannan runduna ta ’yan sanda ke ta kokari ba ni hadin kai wajen cimma  irin manufar da nake da ita na tabbatar da ganin cewa baya ga rashin tsoma baki a harkar siyasa ko nuna son zuciya a yayin zaben 2023, ’yan sandan Najeriya za su taka rawa wajen ganin cewa an gudanar da zabukan cikin tsari da kwanciyar hankali ta yadda sakamakon zaben zai kasance karbabbe ga kowanne dan kasa.”

Da yake jawabi yayin bikin, ministan harkokin ’yan sanda na tarayyar Najeriya Muhammad Maigari Dingyadi ya ce nan ba da jimawa ba wasu motocin silke da sauran kayayyakin aiki da aka sayo daga kasar China za su iso Najeriya domin amfani ’yan sandan kasar wajen kara kyautata tsaro a cikin gida.

Daga cikin kayayyakin da aka samarwa sun hada motocin sintiri 88 da motoci masu feshin ruwan zafi guda 10 da motoci masu dauke da na’urorin sansano maboyar ’yan ta`adda guda 21 kana da riguna masu garkuwa  guda dubu 9,607. (Garba Abdullahi Bagwai)