An fara jigilar kayayyakin jin kai da gwamnatin Sin ta samar wa Syria
2023-02-14 14:34:00 CMG Hausa
Da sanyin safiyar yau Talata ne aka fara jigilar kayayyakin jin kai na shawo kan bala’in girgizar kasa, wadanda gwamnatin Sin ta bai wa kasar Syria. An yi hasashen cewa, kayayyakin za su isa birnin Damascus na kasar Syria da safiyar gobe Laraba.
Wadannan kayayyakin jin kai sun kunshi jakukkunan ba da agajin gaggawa dubu 30, da rigunan sanyi dubu 10, da tantuna 300, da barguna dubu 20, da wasu na’urorin taimakawa numfushi, da injunan sa barci, da na’urorin samar da iskar oxygen, da wasu fitilun tiyata da dai sauransu.
Bugu da kari, an kai wasu kayayyakin jin kai da kungiyar Red Cross ta Sin ta bai wa kasar ta Sham a karo na biyu birnin Damascus, fadar mulkin kasar Syria a jiya Litinin.
Tuni dai kayayyakin ayyukan jin kai kashi na biyu da kungiyar Red Cross ta Sin ta bai wa Syria, sun isa birnin Damascus a jiya Litinin. Kuma jakadan Sin dake Syria Shi Hongwei, da mataimakin shugaban hukumar kula da jihohi da hukumar muhallin hallitu na kasar Moutaz Douaji, da sauran jami’ai, sun halarci filin jirgin saman kasar don maraba da su.
An ruwaito cewa, kayayyakin a wannan kashi sun kunshi tantuna, jakukkunan kayan ba da agajin gaggawa, da tufafi, da magunguna, da sauran abubuwan da ake bukata a wuraren da girgizar kasar ta shafa, wadanda za su taimakawa mutane fiye da dubu 10.
Bisa kididdigar farko-farko da tawagar ceto ta Sin ta fitar, ya zuwa ranar 12 ga watan nan, tawagar ceto ta Sin ta riga ta ceto mutane 6 a yankin da bala’in ya shafa sosai, wato birnin Antakya dake lardin Hatay.
Ya zuwa yanzu, tawagar Sin ta riga ta aika da rukunonin ceto guda 13, mai kunshe da jimillar jami’an ceto 206, inda suka ceto mutane 6, tare da gano gawawwakin mutane 8. Ban da wannan kuma, tawagar aikin ceto ta yankin musamman na Hong kong ta Sin, ita ma ta yi nasarar ceto karin mutane 3. (Safiyah Ma)