logo

HAUSA

Mutane 19 sun rasu sakamakon hare-hare a Burkina Faso

2023-02-14 14:00:38 CMG Hausa

Rahotannin da aka fitar a jiya Litinin na cewa, a kwanakin baya bayan nan, a kalla mutane 19 sun rasa rayukan su, sakamakon hare-hare biyu da aka kaddamar a Burkina Faso.

Jami’an hukumar tsaron lardin Koulpelogo na kasar sun bayyana cewa, ‘yan bindiga sun kai wa wani kauye na lardin dake gabashin kasar hari da yammacin shekaran jiya Lahadi, kuma sakamakon hakan, a kalla mutane 12 ciki har da ‘yan aikin tsaro na sa kai guda biyu sun rasa rayukan su, kuma an lalata kayayyakin sadarwa dake wurin.

Ban da haka, wasu rahotanni sun ce wasu ‘yan bindigar sun yi musanyar wuta da ‘yan aikin tsaro na sa kai a lardin Kossi, wanda ke arewa maso yammacin kasar a ranar 9 ga wata, lamarin da ya sabbaba rasuwar mayaka 7.

Kawo yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kaddamar da hare-haren, kuma gwamnatin Burkina Faso, ita ma ba ta fitar da sanarwar mai nasaba da hare-haren ba. (Jamila)