Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama’ar Turkiyya da Syria
2023-02-13 20:10:02 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, bayan aukuwar girgizar kasa a Turkiyya da Syria, Sin tana nuna goyon baya, da samar da gudummawa ga kasashen biyu wajen yaki da bala’in.
Wang Wenbin ya ce kayayyakin agaji da gwamnatin kasar Sin ta turawa Turkiyya a karo na farko, sun isa birnin Istanbul a ranar 11 da 12 ga wannan wata, ciki har da barguna, da tantuna, da sauran kayayyakin da aka fi bukata a yankuna masu fama da bala’in. Kaza lika Sin tana kokarin gudanar da aikin ba da abincin agaji cikin sauri, ciki har da alkama mai nauyin tan 220 da za a kai Syria, baya ga alkama da shimkafa da ta kai tan fiye da dubu 3 da za a kaiwa kasar cikin wannan wata.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya yi kira da cewa, ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta soke takunkumin da aka kakabawa Syria ba tare da bata lokaci ba, da daina yin hayaniyar siyasa, alal misali sassauta takunkumin cikin gajeren lokaci. (Zainab)