Dimbin gine-gine sun rushe a Turkiyya sakamakon mummunar girgizar kasa
2023-02-13 17:39:32 CMG Hausa
Sabbin alkaluman da hukumar kula da iftila’i da agajin gaggawa ta kasar Turkiyya ta fitar a jiya Lahadi sun shaida cewa, sama da gine-gine dubu 20 sun rushe, sakamakon girgizar kasa da ta afkawa kudancin kasar a ranar 6 ga watan nan, lamarin da ya jawo shakku kan ingancin gine-ginen.(Lubabatu)