An bude babban taron samar da ilimi ta na’ura mai kwakwalwa na duniya a birnin Beijing
2023-02-13 14:09:06 CMG Hausa
An bude babban taron samar da ilimi ta na’ura mai kwakwalwa, bisa jigon “gyare-gyaren adadi da makomar aikin ba da ilmi” a yau Litinin a nan birnin Beijing.
Za a gudanar da taron ne na yini biyu ta kafar yanar gizo da zahiri. Kuma wakilai daga kasashe da yankuna 130, sun yi rijistar halarta. Sannan jakadun kasashe kusan 50, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa wadanda suke zaune a nan kasar Sin, da kuma shugabannin wasu shahararrun jami’o’i, na halartar sa a zahiri.
A gun taron, za a yi mu’ammala, da tattaunawa kan yadda za a samu sauye-sauye ta hanyoyin amfani da bayanai daga na’ura mai kwakwalwa, da kokarin bunkasawa, da kuma amfani da bayanai daga na’ura mai kwakwalwa, sannan za a yi kokarin horas da dalibai da malamai dabarun amfani da wannan fasaha. Kaza lika za a tafiyar da harkokin ba da ilimi ta hanyar amfani da bayanan kwamfuta da dai sauransu.
Bugu da kari, a yayin taron, za a fitar da kundin kasar Sin mai kunshe da fasahohin ba da ilmi da fasahohin kwamfuta, da ma’aunin bunkasuwar wannan fanni na ba da ilimi, da fitar da ka’idojin dandalin ba da ilmi ta kwamfuta, da ajandar kafa kungiyar tarayyar sassa masu ba da ilmi ta hanyar kwamfuta ta kasa da kasa, da kuma ajandar ci gaba da hadin gwiwa ta kasa da kasa a wannan fanni.
Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa cibiyar tattara albarkatun ba da ilimi mafi girma a duniya. Ban da wannan, dandalin ba da hidimomi, mai alaka da ba da ilmi ta kwamfuta na kasar, ya riga ya samar da hidimomi ga kasashe da yankuna fiye da 200 a fadin duniya.
Ya zuwa ranar Juma’a 10 ga watan Fabarairun nan, yawan kallon dandalin ya kai sama da biliyan 6.7, kuma yawan masu ziyartar dandali ya kai fiye da biliyan 1.(Safiyah Ma)