Wang Yi zai ziyarci kasashen Faransa da Italiya da Hungary da Rasha tare da halartar taron tsaro na 59 na Munich
2023-02-13 19:50:16 CMG Hausa
Daraktan ofishin harkokin waje, na kwamitin kolin JKS Wang Yi, zai ziyarci kasashen Faransa, da Italiya, da Hungary da Rasha, tsakanin ranaikun 14 zuwa 22 ga watan Fabarairun nan, bisa gayyatar gwamnatocin kasashen 4.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, Wang Yi, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, zai kuma halarci taron karawa juna sani game da tsaro karo na 59, wanda zai gudana a birnin Munich na Jamus, inda zai gabatar da jawabi yayin lokacin da aka warewa Sin a taron.
Ana sa ran cikin jawabin na sa, Wang zai tabo manufofin shugaba Xi Jinping, don gane da fatan cimma cikakkun matakai, na hadin gwiwa masu dorewa, game da tsaron kasa da kasa, wadanda ke fayyace matsayar Sin na goyon bayan samar da ci gaba cikin lumana, da gabatar da matsayin kasar game da muhimman batutuwan da suka shafi kasa da kasa, bisa jigon taron na wannan karo. (Saminu Alhassan)