logo

HAUSA

Asusun UNICEF ya bayar da tallafi domin horas da malamai 18,000 a jahohin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya

2023-02-13 09:23:15 CMG Hausa

A ranar 12 ga wata, a birnin Maiduguri dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, asusun tallafawa kananan yara MDD ya sanar da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi tallafinsa domin bayar da horon watanni 12 ga malaman makarantun firamare dake jahohin Adamawa da Borno da Yobe.

Jami’ar asusun ta UNICEF a jihar Borno Mrs Folashade ce ta tabbatar da hakan yayin wani taron manema labaru domin tattaunawa a game da nasarorin da Shirin hadin gwiwa na duniya kan tallafawa sha’anin ilimi a Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya, wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Jami’ar asusun na UNICEF a jihar Borno ta ce shirin bayar da horon zai taimaka sosai wajen kara inganta sha’anin ilimi a wadannan jihohi guda uku da suka fi fuskantar kalubalen tsaro daga ayyukan ’yan ta’adda tsawon shekaru masu yawa, lamarin da ya sukurkutar da harkokin ilimi a yankunan.

Mrs Folashade ta ci gaba da cewa, kashi 29 ne kawai na adadin malaman da suke koyarwa a jahohin suke da mafi kankantar takardar kwarewa ta malanta, lamarin da yake shafar ingancin ilimin da yara ke samu a makarantun firamare da na sakandire.

Ta ce wannan yunkuri ana yinsa ne bisa hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya da cibiyar horas da malamai da kuma majalissar yiwa malamai rijista ta tarayyar Najeriya.

Mrs Folashade ta ce, bincike ya tabbatar da cewa, adadin yara maza da mata miliyan 1.9 ne tashe-tashen hankulan arewa maso gabashin Najeriya ya hana samun ingantaccen ilimin da ake bukata, wanda ya zama wajibi yanzu a himmatu wajen ceto su daga shiga yanayi na jahilci.

Ta ce za a sami nasarar hakan ne kawai wajen kyautata kwazon malaman ta hanyar ba su horon da ya kamata, inda ta kara da cewa a yanzu haka malami daya ne ke koyar da dalibai 124 a wadannan jahohi guda uku dake shiyyar arewa maso gabas saboda rashin dakunan karatu masu kyau da kuma karancin malaman kansu.

Har’ila yau kuma asusun na UNICEF ya tabbatar da cewa kashi 48 ne kawai na daliban firamaren wadannan jahohi uku suka samu kammala karatun fimare.

“Wasu daga cikin malaman, tashe-tashen hankula ya shafe su sosai, domin wasun su ma sun rasa rayukan su, yayin da wasu daga cikin su kuma sun kauracewa garuruwansu, sabo da haka akwai matukar bukatar a kawowa malaman da suka yi saura tallafi ta hanyar ba su horo domin su kara samun kwarewa a fannin koyarwa domin amfanawar dalibai.”

Madam Folashade ta kuma tabbatar da cewa, baya ga horas da malamai, asusun na UNICEF karkashin shirin hadin gwiwa na tallafin ilimi zai buda kofar karuwar yara da suke shiga makaranta, wanda yanzu haka shirin ke aikin gyara makarantu guda hamsin tare kuma da gina karin dakunan karatu a wadannan jahohi.

Daga tarayyar Najeriya, wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)