logo

HAUSA

Ta yaya za a motsa jiki da kiwon lafiya, a kokarin kara azama kan kyautatuwar lafiyar kwakwalwa?

2023-02-12 07:48:04 CMG Hausa

Motsa jiki yana tabbatar da daidaiton kwakwalwa, ta yadda kwakwalwarmu za ta kasance cikin yanayi mai kyau. Kana motsa jiki na iya rage matsin lambar da ake fuskanta, ta yadda za a kyautata karfin garkuwar jiki. To ta yaya za a samu kyautatuwar lafiyar kwakwalwa ta hanyar motsa jiki?

Masu sha’awar motsa jiki su kan samu saurin gudanar jiki sakamakon motsa jiki bisa matsakaicin karfi, amma idan sun dauki tsawon lokaci suna motsa jiki fiye da yadda suke iya jurewa, to, kila gudanar jiki a jikunansu ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba. Don haka wajibi ne a rika motsa jiki gwargwadon karfi. Haka kuma wasan Yoga, raye-raye, wasan Taiji, wasan kwallon raga da sauran irinsu, wasanni ne masu wuyar gudanarwa, wadanda mutane suke bukatar yin wasannin bisa basira.

Har ila yau, kar a manta, sauri ya kan haifi nawa! A motsa jiki bisa matakai guda 3, wato dumama jiki, motsa jiki ta hanyar sakin jiki. Baligai suna motsa jiki sau 3 a ko wane mako, inda kuma suke daukar mintoci 45 a ko wane karo. Wajibi ne wadanda suka dade suna zaune a kujera a daki su fara motsa iki, su shigar da motsa jiki cikin zaman rayuwarsu ta yau da kullum, kamar yadda suke cin abinci da yin barci a ko wace rana. Idan sun ji dadin sauye-sauyen da za a samu sakamakon motsa jiki, to, hakan zai amfana wa lafiyar kwakwalwarsu. 

Bayan haka kuma, idan ana son tabbatar da lafiyar kwakwalwa, to, a rika motsa jiki ta hanyar da ta dace, kana a tabbatar da kasancewa cikin koshin lafiya a fannin tunani, a rayu yadda ya kamata, a daina shan taba da rage shan giya, a tabbatar da samun isasshen barci, kar a rika yin barci fiye da kima. Saboda sanin kowa ne cewa, lokacin barci, lokaci ne mafi dacewa da kyautata jiki. Idan an dade ana yin barci,ko ba a samu isasshen barci ba, to, kwayoyin halitta dake cikin kwakwalwa za su tsofa cikin hanzari.

Tsoffi da masu matsakaitan shekaru fa? Ya fi kyau su ci abinci ta hanyar kimiyya, su kauracewa cin abinci dake sanya kiba da sukari da man girke, su ci sinadarin furotin da ake samu a dabbobi da na tsirrai yadda ya kamata. Ban da haka kuma, su rika motsa jiki, don samun daidaiton nauyin jiki, sa’an nan yin rigakafin kamuwa da cututtukan magudanar jiki a kwakwalwa yana da muhimmanci gare su. Haka zalika, masu fama da cututtukan magudanar jiki a zuciya da kwakwalwa ya kamata su rika zuwa na yi musu binciken lafiya lokaci-lokaci, su kula da lafiyarsu sosai, su sha sinadarin folic acid bisa umarnin likita, wanda yake amfani wajen rage kamuwa da shan inna.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta bayyana mana cewa, yin mu’amala da al’umma, yana faranta ran mutane. Tsoffi kuma ya fi kyau su rika shiga harkokin al’umma a kullum, su kuma motsa jiki ta hanyoyin yin wasan Taiji, raye-raye da sauran irinsu marasa wahala, wadanda suke amfanawa lafiyar kwakwalwa da zuciya. (Tasallah Yuan)