logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da dan takarar mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima

2023-02-12 16:51:03 CMG Hausa

A ranar Juma’a ne jakadan Sin dake Nijeriya Cui Jianchun, ya gana da dan takarar mataimakin shugaban Nijeriya a jam’iyyar APC mai mulki, kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

A yayin ganawar ta su, jakada Cui ya bayyana cewa, an gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis na Sin karo na 20 a watan Oktoban shekarar bara, kuma bayan haka jama’ar kasar Sin sun kama sabon tafarki na zamanintar da kasa, bisa tsarin gurguzu a dukkan fannoni, kana an kawo sabuwar dama ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma Sin da Nijeriya.

Jakadan ya ce manufofin samun ci gaba na Sin da Nijeriya wato 5GIST, sun inganta imanin siyasa, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da kiyaye tsaro, da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, da kuma mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Nijeriya. Kaza lika Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da Nijeriya, wajen sa kaimi ga inganta hadin gwiwar kasashen biyu, da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.

A nasa bangare, Shettima ya bayyana cewa, Sin ta samar da babbar gudummawa, da goyon baya ga Nijeriya, wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da kuma zamanintar da kasa. Ya ce Najeriya tana matukar godiya ga kasar Sin bisa hakan.

Ya ce hadin gwiwar dake tsakanin Nijeriya da Sin a fannoni daban daban, ya taimakawa Najeriya wajen raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da kuma tabbatar da tsaron kasar, da sada zumunta, da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, matakan da suka dace da bukatun jama’ar Nijeriya. Shettima ya kuma yi imanin cewa, za a kara inganta dangantakar dake tsakanin Nijeriya da Sin, da fadada hadin gwiwarsu baki daya.  (Zainab)