logo

HAUSA

Kenya Ta Karbi Bakuncin Rukunin Farko Na Sinawa Masu Yawon Bude Ido Bayan Annoba

2023-02-12 15:57:13 CMG Hausa

A jiya Asabar ne kasar Kenya ta karbi bakuncin rukunin farko na Sinawa masu yawon bude ido, bayan shekaru 3 da dakatar da hakan, sakamakon bazuwar annobar COVID-19.

Yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka yi domin hakan, a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar, manyan jami’an gwamnatin Kenya, da shugabanni a fannin hada-hadar yawon shakatawa sun hallara, inda suka yi maraba da tawagar ta farko mai kunshe da Sinawa 40, wadda ta taso daga birnin Guangzhou zuwa Nairobi ta jirgin saman kamfanin Southern Airlines.

Yayin bikin, babban sakatare a hukumar lura da harkokin yawon bude ido ta kasar John Ololtuaa ya jinjinawa gwamnatin kasar Sin, bisa yadda ta zabi kasar Kenya cikin kasashen Afirka 3, wato Kenya da Afirka ta Kudu da Masar, a matsayin kasashen da za su karbi bakuncin Sinawa masu yawon shakatawa a nahiyar, bayan kyautata matakan shawo kan cutar COVID-19.

A cewar Ololtuaa, Kenya za ta yi amfani da damar babbar kasuwar Sin wajen bunkasa fannin yawon bude ido, da gaggauta farfado da fannin, wanda ke samar da kaso 7 bisa dari na GDPn kasar.

Jami’in ya kara da cewa, a halin da ake ciki, Sin ce kasa ta 6 a jerin masu samarwa Kenya kudaden shiga ta hanyar yawon shakatawa, inda take samarwa kasar kaso 5.5 bisa dari na jimillar ‘yan yawon bude ido na kasa da kasa kafin bullar annobar COVID-19.  (Saminu Alhassan)