logo

HAUSA

Tai Lulu-Samun ci gaba mai kyau da kasar Sin ke yi, zai ba mu karin damammaki

2023-02-13 19:32:29 CMG Hausa

Tai Lulu da ta fito daga tsibirin Koh Samui na kasar Thailand, ta shafe tsawon shekaru 12 ta na zaune a kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan, ta yi amfani da damar ci gaban kasuwancin irin na yanar gizo tsakanin kasa da kasa, don kara saurin raya sana’arta. Tana cin gajiyar sakamakon bunkasuwar kasar Sin, kuma ta cimma burinta na rayuwa a kasar.

 

A cikin yan kwanakin da suka gabata, Tai Lulu ta shagaltu da tambarin durian da ta kafa tare da abokanta. Tawagarta tana da ma'auni a sarari, wasu suna tuntubar manoma, masu ba da kayayyaki da zirga-zirgar kayayyaki a Thailand, yayin da wasu ke da alhakin neman hanyar sayar da kaya a kasar Sin. Sayar da kaya kai tsaye ta yanar gizo shi ne hanyar tallace-tallace da suka fi so.

Bayan samun kudin tallafi daga gwamnatin kasar Sin a shekarar 2010, sai Tai Lulu ta zo jami'ar Guangxi da ke birnin Nanning a kudu maso yammacin kasar Sin, inda ta samu digiri na biyu da na uku daya bayan daya. Daga baya, ta zama malamar kasashen waje a makarantar, kuma ta kasance matashiya masaniya a fannin tattalin arzikin Sin da ASEAN. Idan ta tuna dalilin da ya sa ta zabi zuwa kasar Sin, za ta gode wa mahaifinta da ya bata shawarar.

 “A lokacin, mahaifina ya dawo daga ziyarar kasuwanci a kasar Sin, ya shaida min cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da ASEAN ko Sin da Thailand za ta karfafa a nan gaba, kuma za a samu karin damammaki, don haka yana fatan zan iya zuwa kasar Sin domin karatu a nan.”

 

Lokacin da Tai Lulu ta zo kasar Sin, an riga an gudanar da bikin baje kolin Sin da ASEAN a birnin Nanning karo na shida. Yayin da ake ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da ASEAN a fannoni daban daban, jama'a da dama daga kasashen ASEAN na zuwa birnin Nanning domin aiki da karatu da kuma zama a nan. Tai Lulu tana jin cewa, Nanning birni ne mai saurin ci gaba, da wayewa da juriya, a nan ake iya samun saurin ci gaban rayuwa.

 “Lokacin da na zo Nanning ba da dadewa ba, birnin yana kokarin samun ci gaba, kuma an soma gine-ginen birane. Amma yanzu a Nanning, akwai jiragen kasa dake karkashin kasa, kekunan haya, da jiragen sama dake zuwa Thailand kai tsaye, gaskiya ana samar da sauki a fannin zaman rayuwa, kuma halin da birnin ke ciki ya yi kama da na kasashen waje. ”

Lokacin da take kasar Thailand, Tai Lulu ta ji cewa, Sinawa suna da himma da gwazo kan aiki da karatu. Ta ce gani ya kore ji, bayan zuwanta kasar Sin, musamman bayan ta zama malama, kwazon da daliban kasar Sin suke nunawa ya burge ta sosai.

 “Ina tsammanin daliban kasar Sin suna dora muhimmanci game da duk abin da suke yi, alal misali, za su duba darasi na gaba da za a koyar kafin lokacin karatu, kuma za su yi bita tare da binciken bayayyan darasin da aka koya musu bayan karatu.”

Irin halin da Sinawa ke ciki shi ma ya kawo tasiri sosai ga Tai Lulu, a ko da yaushe ta kan ingiza kanta don kara koyan ilimi da samun fasahohi sosai, ta yadda za ta iya samun ci gaba mai kyau a kasar Sin.

A shekarar 2020, sakamakon yaduwar annobar COVID-19, Tai Lulu da malaman makarantar suka fara koyar da dalibai ta hanyar watsa shirye-shiryen kai tsaye ta yanar gizo. Har ila yau, ta gano cewa, an kawo cikas sosai a harkokin cinikin shige da fice irin na gargajiya, sakamakon katsewar mu’ammala, amma hanyar sayar da kaya kai tsaye ta yanar gizo ta karya iyakokin da lokaci ke da shi, wadda kuma ta ingiza kasuwa yadda ya kamata.

A farkon shekarar 2021, Tai Lulu da abokanta sun gwada sayar da durian na Tailand kai tsaye ta yanar gizo, kuma sun samu nasara, wanda ya sa ta ga damar kasuwanci na sayar da kaya kai tsaye ta yanar gizo a kasar ta Sin.

Daga baya, ta kuma samu horo a fannin kafa shagon sayar da kayayyaki ta yanar gizo. Tana fatan taimakawa 'yan kasuwan Thailand su kara fahimtar kasuwar kasar Sin da kuma amfani da sabbin damammaki na ci gaban ciniki ta kokarinta.

A matsayinta na malama, Tai Lulu tana shirin taimakawa dalibanta na kasar Thailand dake karatu a kasar Sin wajen samun aikin yi bayan karatu a nan kasar.

 “Suna iya aiki a kamfanonin kasar Sin ko su zama jagororin yawon shakatawa, ko kuma koyar da Sinanci, ko yin kasuwanci da Sinawa kai tsaye. Yanzu sana’ar sayar da kaya ta yanar gizo na samun saurin ci gaba, ana iya gayyatar karin kamfanonin Thailand don su zuba jari a jihar Guangxi, ta hakan daliban da muke horarwa za su iya yin aiki a nan.”