logo

HAUSA

Tanzania ta tsaurara matakan sa ido a iyakokinta yayin da cutar Kwalara ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,200 a Malawi

2023-02-11 17:06:21 CMG Hausa

Hukumomin lafiya a Tanzania, sun ce an tsaurara matakan sa ido a cibiyoyin lafiya da yankunan dake kan iyakar kasar da makwabciyarta Malawi, domin dakile yaduwar cutar Kwalara a kasar ta gabashin Afrika.

Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar Tanzania Abel Makubi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da yake bayani game da rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO dake cewa, cutar kwalara mafi tsanani a tarihin Malawi, ta yi sanadin mutuwar mutane 1,210, yayin da ake fuskantar karancin alluran rigakafi da barkewar cutar a kasashen Afrika da dama.

A cewar WHO, bayan nazartar yanayin yaduwar cutar a kasar Malawi da sauran kasashe makwabta, ta ayyana cutar a matsayin mai tsanani.

Ta kara da cewa, Zambia dake makwabtaka da Malawi, ita ma ta bayar da rahoton samun masu kamuwa da cutar, haka zalika Burundi da Kamaru da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Habasha da Kenya da Nijeriya da kuma Somalia. (Fa’iza Mustapha)