logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta maida martani game da shakkun da ake mata dangane da fashewar bututun Nord Stream

2023-02-11 16:28:16 CMG Hausa

Kwanan nan ne shahararren dan jaridan Amurka, Seymour Hersh ya ruwaito rahoton dake cewa, gwamnatin Biden ta kulla makarkashiyar lalata wani bututun da ake kira Nord Stream Pipeline, wanda kasar Rasha ke amfani da shi don jigilar iskar gas dinta zuwa kasashen Turai. Duba da kasancewarsa kwararre kuma fitaccen dan jaridan a bangaren yada labaran Amurka, gami da bayanai filla-filla masu dimbin yawa da ya wallafa a rahotonsa, ana ganin cewa rahoton nasa gaskiya ne, duk da cewa kwamitin tsaron kasa na fadar White House, da hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka wato CIA, da ma’aikatar harkokin wajen kasar, dukka sun musunta. A cewarsu, babu gaskiya a rahoton Hersh ko kadan. Su kuma manyan kafafen yada labaran kasashen yamma bu su ce uffan ba game da wannan labari.

Sama da watanni hudu da suka gabata, bututu biyu da Rasha take amfani da su don jigilar iskar gas zuwa Jamus, wato “Nord Stream-1” da “Nord Stream-2” sun yi yoyo a wani yankin teku dake kusa da kasashen Sweden da Denmark, inda tashar bincike ta Sweden ta gano cewa, bututun da ya yi yoyo ya samu fashewa mai karfi a karkashin ruwan teku. Bangarori daban-daban na ganin barna ce da aka yi da gangan, musamman lokacin da ake samun kazantar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, gami da tsawwalar farashin makamashi a duniya.

Bututun iskar gas na Nord Stream, muhimmin aikin more rayuwar dan Adam ne da aka gina tsakanin kasa da kasa. Lalacewarsu ya kawo babbar illa ga kasuwar makamashi gami da muhallin halittun duniya, don haka dole a hukunta wadanda suka aikata laifin lalata shi. A halin yanzu, rahoton binciken da dan jaridan Amurka Hersh ya wallafa, yana taimakawa sosai wajen binciken musabbabin lamarin, wanda kamata ya yi bangarori daban-daban su mayar da hankali a kai.  

Haka kuma, ya zama dole Amurka ta maida martani game da shakkun da kasa da kasa ke mata, da bada hadin-kai don binciken musababbin aukuwar lamarin, saboda duniya na bukatar adalci da sanin gaskiya. (Murtala Zhang)