logo

HAUSA

Za`a yi aikin kidayar jama`a a Najeriya daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu

2023-02-10 09:54:38 CMG HAUSA

 

A ranar Alhamis 9 ga watan, shugaban hukumar kidayar jama’a a tarayyar Najeriya Alhaji Nasiru Isah Kwara ya tabbatar da cewa, aikin kidayar da za a gudanar a kasar cikin watan gobe zai zarta sauran ayyukan da aka gudanar a baya ta fuskar samar da sahihan bayanai da za su samu  karbuwa ga kowanne jinsin al’ummar kasar.

Shugaban ya tabbatar da hakan ne a Abuja lokacin da yake jawabi wajen taron ’yan jaridu karo na 24 da jami’an gwamnati ke zayyano irin nasarorin da gwamantin shugaban Muhammadu Buhari ta samu a tsawon shekarun mulkinsa.

 Shugaban hukumar kidayar jama’ar ta tarayyar Najeriya ya ce, sabo da irin goyon bayan da shugaban kasar yake bayarwa kan duk wasu al’amura da suka shafi hukumar, akwai kyawawan alamu dake nuna cewar, aikin kidayar na bana zai gudana cikin tsari irin yadda yake wakana a kasashen duniya.

Ya tabbatar da cewa sakamakon shirin da hukumar ta yi, ba za a bar ko da mutum daya ba, ba tare da an kirga shi ba, saboda yadda aka sake fasalin aikin kidayar, da kwarewar ma’aikatan da za su gudanar da aikin kana da nau’ikan kayan aikin da aka yiwo oda.

Alhaji Nasiru  Isah Kwara ya sanar da cewa na’urorin fasaha guda 4 da hukumar za ta yi amfani da su a aikin kidiyar ba wai aikin su zai takaita ga samar da adadin alkaluman jama’a ba ne, za kuma su samar da karin wasu bayanai na musamman da za su taimakawa gwamanti da al’umma wajen tsara manufofi da ayyukan ci gaban rayuwa.

Shugaban hukumar kidayar jama` ar ta tarayyar Najeriya ya kuma sanar da cewa za a ci gaba da kidayar magidanta da iyalansu da kuma gidaje da ma duk wanda yake zaune a kasar lokaci zuwa lokaci bayan kammala aikin kidayar na gama gari da za a fara daga ranar 29 ga watan gobe zuwa 2 ga watan Afrilu.

“Wayar da kan mahimmai daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar kidayar domin neman hadin kansu wajen tabbatar da nasarar aikin abu ne da ya zama wajibi, sannan kuma hakkin duk wanda yake cikin tsarin ne ya yi amfani da harshen da al’umma za su fahimce shi ta yadda za su samu kwarin gwiwar shigowa su ba da tasu gudumawar kan nasarar aikin.”

Ya ce duk wasu ayyukan raya kasa, ana samun nasarar su ne bayan an yi la’akari da adadin yawan al’ummar da ake da su, saboda haka akwai bukatar jama’a sun bayar da dukkan hadin kai da ya kamata ga jami’an kidaya idan sun ziyarci yankunan su.

A bisa dai yadda doka ta tanadar ana gudanar da kidayar jama’a ne a Najeriya a duk shekaru goma, amma yanzu an shafe shekaru 17 ba a gudanar da kidayar ba, lamarin da shugaban hukumar ke alakantawa da matsalolin tsaro da tattalin arziki da kuma annobar Covid-19.

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai. CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)