logo

HAUSA

Mutane 18 suka mutu sakamakon cutar sankarau a Nijar

2023-02-10 09:41:01 CMG HAUSA

 

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS ta sanar da bullowar cutar dan sankarau fiye da yadda aka san ta a Nijar. A cewar kungiyar, annobar ta kashe mutane 18 tun cikin watan Nuwamban shekarar 2022, tare da nau'in sumfurin kwayar cuta mai suna "nau’in C na ciwon sankarau", a cewar wani rahoton binciken cutuka na kungiyar OMS. Haka kuma kungiyar ta bayyana cewa akwai yiyuwar bazuwar wannan cuta sannu a hankali zuwa kasashen shiyyar yammacin Afrika, musamman ma a tarayyar Najeriya inda aka annobar nau'in irin wannan cuta. Tuni dai kungiyar OMS tare da hukumomin kiwon lafiya na Nijar sun shirya wasu kamfen shaushawa tare da alluran cutar dan sankarau fiye da dubu shida. (Mamane Ada)