logo

HAUSA

WHO ta nuna damuwa kan cutar kwalara a Afrika

2023-02-10 13:07:48 CMG HAUSA

Ofishin kula da harkokin Afrika na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya kira wani taron manema labarai ta kafar bidiyo a jiya, a Brazavilla hedkwatar Jamhuriyar Kongo, inda jami’i mai kula da matsaloli masu tsanani na ofishin ya nuna cewa, yanzu haka cutar kwalara ta lahanta mutane a kasashe 18 na duniya.

Kasashen da lamarin ya fi shafa su ne Mozambique, da Zambiya, da Kamaru, da Najeriya, da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, da Burundi, da Kenya, da Malawi, da kuma Habasha.

Jami’in WHOn ya ce idan wannan yanayi ya dore, tsarin kiwon lafiya na wadannan kasashe zai fuskanci matukar matsin lamba, kuma zai kawo kalubale ga tsarin kandagarkin annoba na duniya. (Amina Xu)