logo

HAUSA

INEC:babu wani abu da zai sanya ta dage gudanar da babban zabe cikin wannan watan

2023-02-09 13:23:45 CMG HAUSA

 

A ranar Laraba 8 ga wata, hukumar zaben Najeriya INEC ta kara tabbatarwa ’yan kasa cewa babu wani dalili ya zuwa yanzu  zai sanya ta gaza gudanar da zabuka cikin wannan watan da kuma watan gobe na Maris.

Shugaban hukumar farfesa Mahmud Yakubu ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai dake fadar shugaban kasa, jim kadan da kammala taron majalissar ministocin kasar wanda ya samu halarta.

Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //

 

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ya shiga taron majalissar zatarwar kasar ne wanda ta saba gudanarwa a duk mako domin yi mata cikakken bayani game da inda aka kwana a shirye-shiryen gudanar da babban zaben kasar wanda ya rage kasa da makonni uku.

Taron na wanann makon, an gudanar da shi ne karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Farfesa Mahmud Yakubu ya ce, ya sanar da taron majalissar zartarwa dukkannin tsare-tsaren da hukumar ta yi a halin yanzu duk da kalubalolin da ake fuskanta yanzu haka a kasar  wadanda suka kunshi  karancin man fetur da kuma batun sauyin kudade.

Ko da yake shugaban hukumar zaben ya ce, dukkan wadannan matsalolin, an rigaya an shawo kan su bayan da hukumar ta samu ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a wadannan bagarori.

Farfesa Mahmud Yakubu ya ci gaba da cewa kamfanin mai na kasa ya ba da tabbacin samar da mai a dukkannin runbunan ajiyar mai na musamman da aka samar a fadin kasar domin motoci za su rinka jigilar ma`aikata da kayan aiki.

“Abu na biyu kuma shi ne batun sauyin kudade, wanda a ranar Talata da ta gabata na zauna da gwamnan babbban bakin Najeriya inda shi ma ya tabbatar mun da cewa ba za mu fuskanci wata matsala ba, kasancewa ma dukkan asusun da hukumar zaben ke amfani da su a jihohi da tarayya suna karkashin kulawar babban bankin  kasar ne.”

A sabo da haka hukumar zaben ta kasa ba ta da wani abu da yake daga mata rai a game da zabukan da za a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabarailu da kuma 11 ga watan gobe na Maris.

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)