logo

HAUSA

Hadin-gwiwar Sin da Australiya ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci ya dace da moriyarsu

2023-02-09 21:21:39 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, Shu Jueting ta amsa tambayar da ta shafi hadin-gwiwar kasarta da kasar Australiya a fannin tattalin arziki da kasuwanci a yau Alhamis, inda ta ce, hadin-gwiwar kasashen biyu ta dace da alfanun daukacin al’ummominsu.

Shu ta ce, kasar Sin na fatan kara tuntubar Australiya, game da wasu batutuwan fasaha ta fannin kasuwanci da suke jan hankalinsu dukka, don lalibo bakin zaren daidaita matsaloli bisa cimma moriya tare. Har wa yau, kasar Sin na fatan Australiya za ta kara hada kai da ita, don kirkiro wani budadden yanayin kasuwanci mai adalci kuma ba tare da nuna bambancin ra’ayi ba ga kamfanonin kasar Sin, don samar da ci gaba ga hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin tattalin arziki da kasuwanci. (Murtala Zhang)