Ya kamata Amurka ta sauya mahangar ta game da Sin
2023-02-09 18:57:12 CMG Hausa
Ga duk mai bibiyar kalaman wasu ’yan siyasar Amurka, ba zai rasa jin kalamai dake bayyana kasar Sin a matsayin abokiyar hamayya ko taraka da ya wajaba Amurka ta takawa birki ba. A daya hannun kuwa, kasar Sin ta sha bayyana wannan mahanga ta Amurka a matsayin kuskure, tare da nanata kira ga Amurka da ta rika kallon alakar dake tsakanin kasashen biyu sama da batun takara kadai, domin kuwa a matsayinsu na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, Sin da Amurka na iya gudanar da hadin gwiwa da cudanya mai tsafta, ba tare da shiga takun saka ko fito na fito ba.
Karkashin matakan da Amurka ke dauka, na bayyana adawa a zahiri ga Sin, an ga yadda take yin matsin lamba ga halastattun hakkokin wasu kamfanonin Sin, tare da kakkaba musu takunkumai, inda a wasu lokutan hakan kan kawo tsaiko ga tsarin samar da hajojin masana’antu na duniya.
Ko da yake shugabannin Amurka a wasu lokacin kan ce ba su da nufin haifar da tashin hankali tsakaninsu da bangaren Sin, amma matakai na zahiri da suke dauka na sabawa hakan, musamman duba da cewa, har kullum Amurka tana jaddada aniyar nan ta “Sanya bukatu da muradun kasar gaban komai”, ba tare da la’akari da bukatar wanzar da daidaito da lura da bukatun sauran sassan duniya ba.
Ko shakka babu duniya na da fadin da kasashen biyu za su iya aiwatar da dukkanin matakan raya kansu yadda ya kamata, ba tare da sun hari juna, ko sun shiga cacar baka maras amfani ba. Kazalika wanzar da kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Amurka, zai kare moriyar al’ummunsu baki daya, tare da burikan da sauran sassan kasa da kasa suke fatan ganin an cimma.
Yayin da kasar Sin ke ta kokarin ganin ta inganta alakarta da Amurka, karkashin manufofin martaba juna, da kaucewa mummunar takara, da zama da juna lami lafiya, da gudanar da hadin gwiwa don cimma moriya tare, ya kamata a nata bangare ita ma Amurka ta yi watsi da ra’ayin nan na “Ko na samu ko kowa ya rasa”.
Bugu da kari, dukkanin wata nasara da kasashen 2 za su samu, za su kasance damammaki na bunkasar dukkanin sassan duniya, don haka ya zama wajibi Amurka ta sauya mahangarta game da Sin, ta kalli Sin a matsayin abokiyar cudanya da za a yi tarayya da ita wajen wanzar da ci gaba mai ma’ana. (Saminu Alhassan)