logo

HAUSA

Layin dogon Habasha zuwa Djibouti ya bunkasa fannin shige da fice na hajoji a Habasha

2023-02-09 11:03:55 CMG HAUSA

 

Gwamnatin Habasha ta ce layin dogo da kasar Sin ta gina da ya hada kasashen Habasha da Djibouti, ya tallafawa sashen shige a ficen hajoji a Habasha.

Wata sanarwar da ma’aikatar sufuri da hidimomin aikewa da sakwannin kasar ta fitar a jiya Laraba, ta ce layin dogon ya taka muhimmiyar rawa, wajen bunkasa nau’ika da adadin hajojin da ake sufurinsu, wanda hakan ya fadada damar shige da ficen hajoji kasar dake gabashin Afirka, inda adadin ya karu daga kaso 11 bisa dari, zuwa kaso 15 bisa dari a kasa da shekara daya.

Da yake karin haske game da hakan, karamin ministan ma’aikatar Denge Boru, ya ce layin dogon ya taimaka matuka, wajen rage lokacin gudanar da hidimomin aikewa da kayayyaki, da tsadar aikin, ta hanyar samar da hadimomi masu inganci ga masu fitar da hajoji daga Habasha zuwa kasuwannin kasashen waje.

Har ila yau, Mr. Boru ya ce layin dogon ya samar da karin zarfi na safarar kayayyakin sarrafawa da ake matukar bukata, don kyautata ayyukan masana’antun Habasha, ciki har da na sarrafa takin zamani. Ya ce layin dogon na taka rawar gani, wajen ingiza ci gaban hidimomin aikewa da kayayyaki a kasar. (Saminu Alhassan)