logo

HAUSA

Masu zuba jari na kara bayyana kwarin gwiwa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin

2023-02-08 09:34:33 CMG Hausa

Yayin da kasar Sin ke kara fayyace matakai daban daban da za ta dauka, domin bunkasa samar da ci gaban tattalin arziki mai armashi, sassa masu zuba jari, da abokan huldarta a fannin cinikayya na kara bayyana kwarin gwiwarsu, da imani kan makomar kasar a fannin bunkasuwa a gida, da ba da gudummawa ga bunkasar ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

A yanzu haka, kasar Sin na aiwatar da matakai daban daban, na bunkasa karfin farfadowa, da daidaita tasirin hajojinta nan da shekarar 2025. Kaza lika kasar Sin na daukar matakan kyautata inganci, da nagartar tattalin arzikinta.

Karkashin manufofin gwamnatin kasar, nan da shekarar 2035, Sin za ta cimma nasarar kafa kakkarfan ginshikin samar da tsarin bunkasuwa mai karko. Irin wadannan manufofi sun sa masu zuba jari daga kasashen ketare kara shigowa kasuwannin Sin, inda a bana, jarin waje na kasar ya yi matukar habaka a manyan kasuwannin shunku na Shenzhen da Shanghai, inda a watan Janairun da ya gabata kadai, darajar hannayen jarin da aka cinikayyar su, ya haura na daukacin shekarar 2022 da ta gabata.

A daya bangaren kuwa, hada hadar da kudaden yuan na Sin na kara fadada, wanda hakan ya faranta ran masu zuba jari. Masu zuba jari da dama na mayar da hankali ga sayen kadarori na kudin Sin, a gabar da suke hangen cewa tattalin arzikin Sin ne zai fara bunkasa a shekarar nan ta 2023.

Kari kan hasashen ’yan kasuwa, shi ma asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya daga mizanin hasashensa ga bunkasar tattalin arzikin Sin a bana, daga kaso 4.4 bisa dari zuwa kaso 5.2 bisa dari.

Masharhanta da dama na cewa, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin a bana, zai kasance karfi da zai dakile koma bayan tattalin arzikin da duniya ke fama da shi. Hakan ya sa IMF ya daga hasashen farfadowar tattalin arzikin duniya a bana zuwa kaso 3.4 bisa dari, sama da kaso 2.9 bisa dari a shekarar 2022.

Bugu da kari, hada-hadar masana’antun sarrafa hajoji dake kara fadada a Sin, da harkokin yawon shakatawa da suka sake budewa, da tafiye-tafiye tsakanin kasar da sauran sassan duniya, dukkaninsu na kara ingiza kwarin gwiwar masu zuba jari na kasa da kasa, ga makomar tattalin arzikin Sin, da ma ci gaban da hakan zai kawo wa tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Hassan, Ibrahim Yaya/ Sanusi Chen)