logo

HAUSA

Gwamnatin DR Congo ta yi tir da harin da aka kaiwa jirgin MONUSCO

2023-02-07 10:51:00 CMG HAUSA

 

Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta yi tir da harin da aka kai wa jirgi mai saukar ungulu mallakin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar wato MONUSCO, ranar Lahadi a wajen Goma, babban birnin lardin Kivu ta arewa.

An kai wa jirgin hari ne ranar Lahadi, lokacin da jirgin ke kan hanyar zuwa Goma daga Beni, wani birni a arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, lamarin da ya kai ga kisan jami’n wanzar da zaman lafiya 1, dan asalin kasar Afrika ta kudu, yayin da sauran suka jikkata.

A cewar MDD, sauran mutanen dake cikin jirgin sun samu nasarar sauka a Goma. Kuma zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Shi ma sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da harin, cikin wata sanarwa a ranar Lahadi. Yana mai cewa, hari kan jami’an wanzar da zaman lafiya na majalisar, laifi ne na yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Ya kuma yi kira ga hukumomi a kasar su gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu ciki. (Fa’iza Mustapha)