logo

HAUSA

Kasar Sin ta kasance mai hangen nesa da samarwa kanta mafita a duk lokacin da ake mata zagon kasa

2023-02-07 17:02:00 CMG Hausa

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da sabbin matakan daukaka tattalin arzikin kasar da ma ingancin kayayyakin da aka kera a kasar.

A yanzu haka, kasar Sin ce babbar mai bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin duniya duk da kalubale da rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Don haka, kara karfafa tattalin arzikinta fiye da yadda yake a yanzu, zai bayar da gagarumar gudunmawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ma kasashe masu tasowa.

A cewar sanarwar da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar jiya, zuwa shekarar 2025, za a bunkasa ingancin kayayyaki kirar kasar Sin. A yanzu haka, kayayyakin kasar Sin sun karade ko ina a fadin duniya, kusan babu gidan da za a shiga ba tare da ganin wani abu da kasar Sin ta kera ba, wannan yana nuna irin nasarar da Sin ta samu wajen kera kayayyaki masu inganci da kuma rahusa. A ganina, hauhawar farashin kayayyaki da aka samu a baya-bayan nan a kasashe masu tasowa har ma da manyan kasashe, na da nasaba da matakan yaki da annobar COVID-19.  Amma bisa la’akari da sabbin matakan da Sin ta dauka, da kuma aka riga aka fara aiwatarwa a bana, ba makawa, za a samu sauki a fadin duniya, kuma kasashe masu tasowa za su samu damar amfana daga kayayyaki masu inganci da masana’antun kasar Sin za su samar.

Haka kuma sanarwar ta ce, kasar za ta inganta takarar masana’antu. A lokacin da ake kokarin dakile masana’antun kasar Sin ta kowacce fuska, wannan mataki zai kara karfafa musu gwiwa da kara samar musu da dimbin damarmaki a duniya, ta yadda babu wanda zai iya dakile su. Karfin takarar da za su yi da takwarorinsu na duniya, zai kara musu tagomashi da kasuwa da kuma samun karbuwa.

Hakika kasar Sin ta kasance mai hangen nesa a ko da yaushe, inda take samarwa kanta mafita a duk lokacin da ake kokarin dakile ta. Haka kuma ta kan mayar da hankali ne ainun wajen inganta kanta a cikin gida ba tare da kokarin dakile wani bangare ko yin zagon kasa ba. Shi ya sa har kullum take kara samun tagomashi da farin jini a duniya, abun da ya kamata sauran kasashe su nazarta domin su yi koyi da shi don tsayawa da kafarsu da samun ci gaba ba tare da dogaro da wani bangare ba. (Faeza Mustapha)