Suleiman Shafiu Gambo: Burina shi ne in koma gida Najeriya don samar mata da ci gaba
2023-02-07 14:58:21 CMG Hausa
Suleiman Shafiu Gambo, haifaffen jihar Kano ta arewacin Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun aikin likitan kashi a wata jami’a da ake kira da “Central South University” wadda ke birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, malam Suleiman Shafiu Gambo, ya bayyana yadda yake jin dadin mu’amala da ‘yan China, da burin da yake kokarin cimmawa, ta hanyar karatun aikin likita a kasar Sin. (Murtala Zhang)