Kasar Sin ta gabatar da korafi ga ofishin jakadancin Amurka dake kasar game da harin da sojin Amurkar suka kai wa kumbonta
2023-02-06 11:18:46 CMG Hausa

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya bayar da umarnin gabatar da korafi ga ofishin jakadancin Amurka a Sin, a madadin gwamnatin kasarsa, dangane da harin sojin Amurka kan kumbon kasar Sin na farar hula.
Xie Feng ya jaddada cewa, shigar kumbon mara matuki na kasar Sin cikin sararin samaniyar Amurka, kuskure ne da ba a yi tsammanin aukuwarsa ba. Yana mai cewa gaskiya a bayyane take, ba za a iya jirkita ta ba. Sai dai, Amurka ta yi biris da hakan, inda ta nace wajen amfani da karfi kan kumbon na farar hula dake shirin barin sararin samaniyarta, lamarin da ya zama tamkar wuce gona da iri da keta ruhin dokoki da ka’idojin kasa da kasa.
Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin na bibiyar yanayin sosai, kuma za ta kare halaltattun hakkoki da muradun kamfanoninta, da ma mutunci da muradun kasar, har ma da mayar da martani a nan gaba. (Fa’iza Mustapha)
