logo

HAUSA

An samar da damar dawo da zirga-zirga a dukkan fannoni a tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar Sin

2023-02-06 22:01:32 CMG Hausa

Daga yau 6 ga watan nan ne aka bude damar dawo da zirga-zirga a dukkan fannoni a tsakanin yankin musamman na Hong Kong da babban yankin kasar Sin. Bisa wannan mataki, a yanzu babu bukatar kayyade adadin mutane, kuma ba a bukatar yin oda a duk tashoshin kwastam a tsakanin babban yankin kasar da Hong Kong. Kamfanin dillancin labaran Bloomberg ya ce, wannan wani bangare ne na kokarin Hong Kong, na farfado da tattalin arziki da yawon bude ido.

A cikin tsawon lokaci da ya gabata, yaduwar annobar COVID-19 ta yi illa sosai ga tattalin arzikin Hong Kong. A ranar 1 ga watan Fabrairu, sashen kidaya na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ya sanar da kiyasin ci gaba, inda ya ce idan aka kwatanta da na shekarar 2021, GDPn Hong Kong a shekarar 2022 zai ragu da kashi 3.5% a zahiri.

Bisa ingantuwar manufofin rigakafin annobar da sauye-sauyen yanayin da kasar Sin ke ciki, a karshe an samar da damar dawo da zirga-zirga a dukkan fannoni a tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar Sin.

Shugaban sashen kudi na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong Chen Maobo, ya bayar da sharhi a ranar 5 ga wata cewa, ana iya sa ran ayyuka daban-daban na kasuwanci, da yawon bude ido da sauran harkokin tattalin arziki za su samu farfadowa cikin sauri, inda ta hakan za a habaka shige da fice, da zirga-zirgar kayayyaki, da yawon bude ido, da dillanci da masana'antar abinci.

Shafin yanar gizo na CNN ya ruwaito rahoton manazarta daga kamfanin Goldman Sachs a ranar 3 ga wata na cewa, ana sa ran bunkasuwar tattalin arzikin Hong Kong zai kai kashi 3.5% a bana. (Mai fassara: Bilkisu Xin)