logo

HAUSA

Sinawa masu zuba jari na da kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Ghana

2023-02-06 10:48:56 CMG Hausa

Shugaban kungiyar al’ummar Sinawa mazauna kasar Ghana, Tang Hong, ya bayyana cikakken kwarin gwiwar da suke da shi kan kasuwar kasar Ghana, duk da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar ta yammacin Afrika.

Tang Hong, ya bayyana haka ne yayin bikin kaddamar da sabon shafin yanar gizo na harkokin kasuwanci na Sinawa a Ghana.

A cewarsa, tabarbarewar yanayin kasuwanci da hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar kudi suka ta’azzara, ta kawo matsaloli ga harkokin kasuwanci na Sinawa.

Ya kara da cewa, duk da tarin wahalhalun da kalubale, yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu, wato Sin da Ghana, ya karu cikin farkon watanni 11 da suka gabata, kuma adadin Sinawa mazauna kasar masu regista, ya karu fiye da na kowacce kasa.

Tang Hong ya ce, dukkan alamu sun nuna cewa, Sinawa masu zuba jari na da cikakken kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Ghana. (Fa’iza Mustapha)