logo

HAUSA

MDD ta yi tir da mummunan harin da ya yi sanadin rayuka 27 a Sudan ta Kudu

2023-02-06 10:27:55 CMG Hausa

Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS), ya yi tir da mummunan rikicin da ya auku a gundumar Kajo-Keji na jihar Central Equatoria ta kasar Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 27 da raunatar wasu da dama a ranar 2 ga wannan wata.

Nicholas Haysom, manzon musamman na sakatare janar na MDD a Sudan ta Kudu, ya yi kira ga hukumomi a kasar da su gaggauta kaddamar da bincike domin hukunta masu laifi.

Cikin wata sanarwar da ya fitar jiya a Juba, Nicholas Haysom ya ce wannan rikici ba abu ne da za a lamunta ba, kuma ya saba da sakon zaman lafiya na ziyarar fafaroma a kasar, wanda ke kira da tabbatar da zaman lafiya da yin sulhu. (Fa’iza Mustapha)