logo

HAUSA

Kyautatuwar matakan kandagarkin COVID-19 sun taimaka wa ‘yan kasuwa baki maza da mata wajen dawowa birnin Yiwu don kasuwancinsu

2023-02-06 15:41:35 CMG Hausa


Nailah, ‘yar kasuwa ce dake da shaidar ‘yar kasa ta Jamus da Italiya. A farkon watan Janairun bana, ta dawo garinta na biyu, wato birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wanda ake kiransa da Baban Shagon Duniya. Jim kadan da saukar ta daga jirgin sama, Nailah ta nufi babbar kasuwar kasa da kasa ta Yiwu ba tare da bata lokaci ba, domin haduwa da abokan kasuwancinta da ba su hadu da juna ba a tsawon shekaru biyu.

Nailah ta fara kasuwancinta a birnin a shekarar 2017, inda hajoji iri daban daban, da aikin rarraba kayayyaki cikin sauki, da kyakkyawan muhallin kasuwanci, suka ba ta babbar damar habaka kasuwancinta.

Hakika dai, dimbin ‘yan kasuwa baki sun dawo kasar Sin kamar yadda Nailah ta dawo, bayan kasar Sin ta daidaita, da kyautata matakan kandagarkin annobar COVID-19, musamman ma a fannin manufar shige da fice.

A ranar 8 ga watan Janairu, wato ranar farko da Sin ta daidaita manufar shigowa kasar daga ketare, kididdigar da aka samu daga filin jirgin saman Yiwu ta nuna cewa, yawan jiragen saman da suka tashi da wadanda suka sauka a ranar ya yi daidai da na kafin abkuwar cutar COVID-19.

Birnin Yiwu, wanda ya shahara wajen kasuwanci yana da alakar cinikayya tare da kasashe da yankuna guda 232, kuma jimillar cinikin waje na birnin ya zarce kaso 65 cikin dari bisa na jimillar GDPnsa. Kafin abkuwar annobar, yawan ‘yan kasuwa baki dake zaune a birnin ya kai kimanin dubu 15, yayin da yawansu da ke zuwa birnin don kasuwanci ya zarce dubu 500 a ko wace shekara.

Amma sakamakon annobar da ake fama da ita a duk fadin duniya, yawan ‘yan kasuwa baki da ke zaune a birnin ya ragu zuwa rabi. Bisa sabuwar kididdigar da hukumar kula da shige da fice ta ofishin ‘yan sanda na birnin Yiwu ta bayar kwanan nan, an ce, ya zuwa yanzu, yawan ‘yan kasuwa baki da ke zaune a birnin ya riga ya zarce dubu 10, kana jimillar tana ta karuwa.

Idan ana yawo a titunan da ke yankin kasuwanci a birnin Yiwu, za a iya gano cewa, a cikin wurin shan kofi da na nishadi, ‘yan kasuwa baki masu tarin yawa suna sha, suna yin hira da abokan cinikinsu. Haka kuma, a ofishin tafiyar da harkokin shige da fice na birnin, ana iya ganin yadda ‘yan kasuwa da dama da ke zuwa don gudanar da harkokin waje, kamar neman samun biza da dai sauransu.

Muhammad, dan kasar Jordan ne da ke kula da wani kamfanin cinikin waje a birnin Yiwu, ya kuma riga ya kafa matsuguni a birnin, bai koma garinsa ba a cikin wadannan shekarun da suka wuce. A ganin wasu ‘yan kasuwa masu son sayen kayayyaki kirar Sin, Muhammad ya san komai game da Sin. Ya tabbatar da cewa, karin ‘yan kasuwa baki za su dawo bayan lokacin hutu na bikin bazara na Sinawa, ganin yadda abokansa suke ta yi masa tambayoyi kan yanayin da Sin ke ciki. Ban da wannan kuma, ya ce, abokansa da dama, sun riga sun sayi tikitin jiragen sama don zuwan kasar Sin bayan bikin bazara. Hakan ya sa Mohammad yin imani sosai ga sabuwar shekara, ya ce, ya zuwa yanzu ya riga ya samu oda da darajarsu ta zarce Yuan miliyan 40, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 5.9.

Bugu da kari kuma, gwamnatin birnin Yiwu ta fara daukar matakai domin karfafa zukatan ‘yan kasuwa baki dawowa birnin. A ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2022, birnin Yiwu ya bayar da matakai goma ta fuskar hidimomi, don kyautata muhallin kasuwancinsa, sa’an nan za a kaddamar da aiwatarwa a bana. Wadannan matakai sun kunshi fannonin ba da sauki ga baki wajen aiki da zama, da harkokin kasuwanci, da hidimar doka, da kafa unguwar kasa da kasa, da ba da aikin jinya ga baki, da karfafa zukatan baki wajen raya aiki, da bayar da labarai da dai sauransu, a kokarin daga matsayin ba da hidimomi ga baki, da kara kwarin gwiwar baki wajen yin kasuwanci da zuba jari a birnin Yiwu.

Kyautatuwar matakan kandagarkin cutar COVID-19 da kasar Sin ke aiwatarwa, ba kawai ya faranta ran ‘yan kasuwa baki sosai ba ne, har ma ya karfafa zukatan ‘yan kasuwa Sinawa dake birnin Yiwu.

Lu Rongqing, dan kasuwa ne dake sayar da kayayyakin wasan yara a birnin, ya kuma bayyana cewa, daga watan Disamban shekarar 2022, yawan oda ya karu a bayyane. Cikin ‘yan kwanaki kawai, yawan odar da ya samu ya zarce na wata guda, wadanda darajarsu ta kai fiye da kudin Sin Yuan miliyan shida, kwatankwacin dalar Amurka dubu 885 a ko wane wata. Ya kara cewa, “bayan abokan cinikinmu sun zo shagona sun gane wa idanunsu samfurin kayayyakin wasan yara, suna iya tabbatar da yawan kayayyakin da za su bukata, sai kuma tsara aikin samarwa yadda ya kamata. Lamarin da ya kara kwarin gwiwata sosai.”

Ban da Lu Rongqing, ayyukan kasuwancin sauran ‘yan kasuwa su ma sun samu farfadowa. A cikin shagon Liu Junming, dan kasuwa mai sayar da kayayyakin wanka, wasu ma’aikatansa na fama da aikin tuntubar abokan cinikinsu da kwamfuta, yayin da wasu ke shirya shirin bidiyon kai tsaye, inda su kan yi amfani da harsuna daban daban wajen yin bayani kan sabbin manufofin shige da fice na kasar Sin, tare da ba da shawarwari kan zuwa kasar Sin. Liu Junming ya bayyana cewa, ko da yake yawan sabbin abokan cinikinsa yana ta karuwa a cikin wadannan shekarun da suka gabata, sakamakon raya kasuwanci a yanar gizo, amma a cikin abokan cinikinsa fiye da 1300, kaso 95 cikin dari bai hadu da su fuska da fuska ba. Yanzu, Liu Junming ya riga ya tattauna da yawancin abokan cinikinsa wajen haduwa da juna a birnin Yiwu bayan bikin bazara. Yayin da yake kokarin gayyato abokan cinikinsa, shi da tawagarsa suna kokarin kago sabbin kayayyaki. Liu ya ce, “tabbas ne za su yi mamaki da gamsuwa, bayan sun zo wurinmu.”

Kamar yadda Sinawa kan ce, tsuntsayen da ke tashi da sassafe na da abinci. Xu Xiaobao, dan kasuwar da ke sayar da kayayyakin ado a birnin Yiwu, a yanzu yana shirin zuwa lardin Guangdong da sauran wuraren kasar Sin don sayen na’urori da yin binciken kasuwa. A ganinsa, tabbas za a samu takara sosai bayan fara kasuwanci, bayan lokacin hutu na bikin bazara, don haka dole ne a tsara shiri tun da wuri, don share fage a fannonin tsara fasali da kayayyaki. Xu Xiaobao ya bayyana cewa, gaskiya ya gamu da matsala wajen kasuwancinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata sakamakon cutar COVID-19.

A shekarar 2022, gwamnatin birnin Yiwu ta soke kudin hayar daki har na tsawon watanni shida ga dukkan ‘yan kasuwa da ke cibiyar kasuwar Yiwu, lamarin da ya taimaka musu sosai. An ce yawan kudin hayar dakuna da aka soke gaba daya, ya wuce kudin Sin Yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 147. Irin wannan taimako ya ba ‘yan kasuwa kwarin gwiwar dagewa. Kaza lika an ce a shekarar 2022, yawan ‘yan kasuwa da ke ci gaba da gudanar da ayyukan kasuwanci a cibiyar ya kai kaso 87 bisa dari.

Otal da dakunan sayar da abinci na birnin Yiwu, su ma suna jin farfadowar kasuwanci. Madam Xu Manlan, mai kula da wani dakin cin abincin kasar Nepal ta bayyana cewa, a jajiberin sabuwar shekarar 2023, wurinta cike yake da ‘yan kasuwar gida da waje, sai da ta kai har zuwa karfe 3 na daren ranar kafin tashi daga aiki. Lamarin da ya sa ta yi Imani sosai ga kasuwancinta a nan gaba.

Yanzu ana lokacin bazara a kasar Sin. A ganin Sinawa, lokacin bazara na alamta farfadowar rayuka da fata. Sakamakon kyautatuwar manufofin kandagarkin cutar COVID-19, harkokin kasuwancin kasar Sin za su kara samun farfadowa, lamarin da zai kara azama ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wanda zai ci gaba da bayar da gudummawa ga karuwar tattalin arzikin duniya.

To kamar dai yadda akan ce ”Laifin dadi karewa”, masu sauraro, a nan shirinmu na yau na “In Ba Ku Ba Gida” ya kammala, da fatan kun karu. Ni Kande da na shirya muku shirin kamar yadda kuka ji shi, nake cewa a kasance lafiya daga nan birnin Beijing. (Kande Gao)