logo

HAUSA

MDD ta bayyana bukatar raba arzikin kasar Libya bisa adalci

2023-02-06 11:03:18 CMG Hausa

Manzon musamman na MDD a Libya, Abdoulaye Bathily, ya jaddada muhimmanci dake akwai wajen raba arzikin kasa cikin adalci a Libya.

Abdoulaye Bathily ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da firaministan Libya Abdul-Hamed Dbeibah a birnin Tripoli, inda suka tattauna kan hanyoyin kawo karshen kiki-kakar siyasa da shirya babban zaben kasar a bana.

Jami’in na MDD ya kuma bayyana cewa, samar da kyakkyawan yanayin gudanar da zabukan hakki ne da ya rataya a kan dukkan bangarori. Yana mai cewa ya kamata a fara da kuma samar da kundin tsarin mulki mai karfi. (Fa’iza Mustapha)