Wasannin kankara sun haskaka babbar ganuwar kasar Sin
2023-02-06 10:09:18 CMG Hausa
Albarkacin bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, babbar ganuwar kasar dake birnin Beijing, ta rika haskakawa da fitulu masu ban sha’awa, yayin hutun bikin bazara na bana, a lokaci guda masu sha’awar wasannin kankara da ‘yan wasan zamiya sun gudanar da wasanni yadda ya kamata, a kusa da wurin da hukumar UNESCO ta sanya cikin jerin abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni. Wurin dake da nisan kilomita 2 daga babbar ganuwa, wanda ake kira da “Badaling ski resort” ya cika da masu sha’awar wasannin kankara.
A cewar babban manajan “Badaling ski resort” Yao Yu, "Karkashin jagorancin masu koyar da wasannin kankarar, ‘yan wasa na iya shiga fannoni daban daban, bayan an yi musu gwajin matakin kwarewa, don tabbatar da tsaron lafiyar su yadda ya kamata”.
Shi kuwa wani mai wasan kankara mai suna Wang Da, cewa ya yi “A yanzu, ba kawai an san Badaling saboda babbar ganuwa ba ne kadai, har ma da wuraren dake wurin na wasannin hunturu. Abu ne mai faranta rai, yin wasan kankara a lokacin hutun bikin bazara. Musamman ganin yadda wuraren wasan kankara da dama dake birnin Beijing suka daga matsayin kayayyakin da ake amfani da su a wuraren a shekarun baya bayan nan, inda karin mutane ke shiga a dama da su a wasannin zamiyar kankara."
A ranar karshe ta shekarar 2022, hukumar gudanarwar gundunar Yanqing dake arewa maso yammacin birnin Beijing, ta kaddamar da tsarin kebe yankunan shakatawa 4, da suka tashi tun daga wajen birnin zuwa yankin wasan Olympic na Yanqing, da babbar ganuwa ta Badaling, da wurin wasan kankara na Badaling, da na Shijinglong, wuraren da suka samar da kyakkyawan yanayi na yawon bude ido ga masu yawon shakatawa.
A watan Disambar shekarar 2022 ne aka budewa al’umma cibiyar wasan zamiyar kankara a yankunan tsaunuka ko “National Alpine Skiing Center”, wurin da ya zama daya daga wuraren da aka gudanar da gasar Olympics, da wasan ajin nakasassu na gasar na lokacin hunturu na birnin Beijing da aka yi a shekarar 2022. Wurin wanda ke kayatar da masu wasan zamiyar kankara matuka, na ci gaba da jawo ‘yan wasa dake more kayayyakin da aka tanada, inda suke musayar bidiyon da suke dorawa kan yanar gizo a dandalolin sada zumunta daban daban.
A gandun wasan kankara na Shijinglong kuwa, yara kanana sanye da kayan wasan kankara, da katifun saukaka faduwa masu ado daban daban, suna koyon wasan zamiya daga masu horaswa. Kaza lika an shirya ayyuka daban daban domin nishadantar da iyalai.
Chen Xiaowei, shi ne mataimakin babban jami’in gandun wasan kankara na Shijinglong, ya kuma ce "Tun bayan da birnin Beijing ya yi nasarar lashe damar karbar bakuncin gasar Olympics ta hunturu a shekarar 2015, adadin masu yawon shakatawa dake zuwa wannan gandu na ta karuwa a duk shekara. Yayin da kuma a baya bayan nan aka kyautata matakan yaki da annobar COVID-19 a Sin, sassan wasannin hunturu sun kara bunkasa, musamman ma a lokacin hutu".
A farkon wannan wata, mutane da suka halarci gandun wasan kankara a Nanshan dake wajen birnin Beijing, sun yi ido biyu da tauraron gasar Olympic dan kasar Sin Su Yiming, wanda a gasar Olympics na hunturu da ya gudana a birnin Beijing a shekarar 2022, ya lashe lambar zinari a Nanshan din, inda ya nuna dabaru da fasahohin wasan kankara masu kayatarwa.
A cewar babban manajan gandun wasan kankara na Nanshan Hu Wei "Tun kafin a cika shekara daya da kammala wasannin Olympics na hunturu da aka yi a kasar, Sinawa na kara mayar da hankali sosai ga wasannin hunturu, wadanda a yanzu suke ta kara habaka.
Kaza lika a gandun wasan kankara na Mengqiyuan wato “Mafarin Buri” da Hausa, wanda ke gundumar Yanqing, matasa na samun horon wasan zamiyar kankara, kan allunan zamaniya masu taya, kafin su koma amfani da takalman zamiyar kankara masu kaifi, wannan tsari an kyautata shi a shekarar 2022 da ta gabata.
Wani mai horas da ‘yan wasa a Mengqiyuan mai suna Yu Yongjun, ya ce "A watan da ya gabata, ‘yan wasan kungiyar matasa masu wasan zamiya ta gajeren zango sun koma samun horo da suka saba. Wasan zamiyar kankara na iya zama abun sha’awa ga yara, da kwararru, kai har ma da masu son mayar da shi sana’a”.
A cewar hukumar kula da wasanni ta birnin Beijing, akwai sama da wuraren wasan zamiyar kankara na alluna sama da 80, da na takalma masu kaifi sama da 30 a sassa daban daban na birnin, wanda hakan ya zama wani jigo mai karfi na horas da sabbin ‘yan wasa a fannin wasannin hunturu.
Yayin karuwar tafiye tafiye na lokacin bikin bazara da ya gabata, layin dogo mai sauri na Beijing zuwa Zhangjiakou, wanda aka yi amfani da shi yayin gasar Olympics, da ajin nakasassu na gasar da birnin Beijing ya karbi bakunci a bara, a yanzu yana samun karuwar masu zuwa domin shiga wasannin zamiyar kankara.
Wang Xiaoyong, shi ne babban jami’i mai lura da tashar jirgin kasa ta Qinghe dake birnin Beijing, ya ce "Masu yawon shakatawa daga birane daban daban, kamar Beijing, da Shanghai, da Shenzhen da Harbin suna zuwa wasan zamiya ta layin jirgin kasan mai sauri na Beijing zuwa Zhangjiakou, wanda hakan ke bunkasa karsashin wasannin kankara.