An kaddamar da ayyuka masu yawa a wurare daban daban na kasar Sin don murnar bikin kunna fitilu na gargajiyar kasar
2023-02-05 16:52:02 CMG Hausa
Yau Lahadi 5 ga watan nan, ita ce ranar bikin “Yuanxiao” wato ranar 15 ga watan farko bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. Bikin Yuanxiao, wanda kuma aka fi sani da bikin kunna fitilu, shi ne muhimmin bikin gargajiyar Sinawa na farko bayan bikin bazara.
Kamar sauran bukukuwan gargajiyar kasar, bikin kunna fitilu shi ma yana da al'adun gargajiya da yawa, a yayin bikin, Sinawa suna yin rawan dragon da ta zakuna, suna kallon fitilu, suna amsa kacici-kacici, suna cin mulmulallen garin shinkafa mai yauki, wato Yuanxiao, ko kuma curin shinkafa, kuma suna jin dadin bikin tare.
A yayin bikin, ana gudanar da ayyuka daban-daban a duk fadin kasar Sin cikin walwala. (Mai fassara: Bilkisu Xin)