logo

HAUSA

WHO ta yi kira da a kara azamar dakile rasa rayuka sakamakon kara bazuwar cutar daji a Afirka

2023-02-05 16:40:36 CMG Hausa

Albarkacin ranar yaki da cutar sankara ko daji ta kasa da kasa, wadda aka yi bikin ta a jiya Asabar, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira ga sassan kasashen yankin kudu da hamadar saharar Afirka, da su lalubo dabarun sanya ido, da ganowa, da ba da jinya kan lokaci, la’akari da karuwar al’ummun shiyyar dake rasa rayukan su sakamakon matsaloli masu alaka da cutar ta daji.

Da take tsokaci game da wannan batu, daraktar WHO ta shiyyar Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya Matshidiso Moeti, ta ce cutar daji na kara matsin lamba ga tsarin kiwon lafiyar al’umma, baya ga kalubalen da tsanantar fatara da rashin daidaito ke haifarwa a shiyyar.

Kaza lika Moeti ta ce a duk shekara, ana samun karin mutane miliyan 1.1 dake harbuwa da cutar, yayin da wadanda cutar ke hallakawa a Afirka suka kai kimamin 700,000, wanda hakan ya haifar da koma baya ga nasarorin da aka samu, a fannin tsawon rayuwar al’ummun nahiyar.

Sai dai duk da haka, Moeti ta ce an cimma manyan nasarori a fannin yaki da cutar daji, inda kasashen Afirka 12 suka kammala tsara matakan yaki da cutar, yayin da karin wasu kasashen suka samar da shirin kasa na kare yara kanana daga harbuwa da cutar.

Ta ce aiki tukuru a fannin jagoranci, ya taimakawa kasashen nahiyar da dama a fannin yaki da cutar, inda tuni kasashen nahiyar 25 suka samar da kyakkyawan tsarin shawo kan ta, yayin da wasu takwarorin su suka tanadi tsarin game aikin ganowa, da jinyar cutar cikin tsarin inshorar lafiyar al’ummun su. (Saminu Alhassan)