logo

HAUSA

An kammala babban taron duniya kan iyakoki masu rauni wanda Najeriya ta karbi bakuncinsa a birnin Abuja.

2023-02-04 18:21:08 CMG HAUSA

 

A ranar Alhamis 2 ga wata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yawaitar iyakoki masu rauni a wasu kasashen Afrika ya taimaka sosai wajen karuwar ayyukan ta’addanci, yaduwar kananan makamai da kuma miyagun kwayoyi a kasashen.

Shugaban yana magana ne a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin sakatare-janaral na kungiyar jami’an lura da kan iyakoki na duniya. 

Kwanaki 3 aka shafe ana gudanar da wannan babban taro kan yanayin iyakoki masu rauni wanda aka kammala ranar 2 ga wata, wakilai 184 da suka fito daga shiyoyi 6 na kasashen  duniya ne suka halarci taron.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, sakamakon wannan yanayi da ake ciki ya zama wajibi Najeriya da kasashen da suke makwaftaka da ita su kara daukar ingantattun matakai na sanya idanu kan iyakokin su.

Ya ci gaba da cewa, taron ya zo dai dai lokacin da Najeriya ke kokarin gudanar da babban zabe wanda ake matukar bukatar kulawa sosai ga iyakokin kasar domin baiwa kowane dan Najeriya damar gudanar da zabensa cikin kwanciyar hankali.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, matsalolin da Najeriya ke fuskanta na yawaitar iyakokin da ba su da kariyar doka yana matukar haifar mata da koma baya a yakin da take yi da masu fasa kaurin miyagun kwayoyi da kananan makamai, lamarin da yake shafar ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa, duk da namijin kokarin da gwamnati ke yi wajen samar da ingantattun kayan aiki ga jami’in hukumar lura da kan iyakoki ta kasar da kuma sauran jami’an tsaro masu kula da shige da fice da dakarun soji, amma ya zama wajibi sauran kasashe su ma su yi koyi.

“Babban fatanmu a nan shi ne taron zai nemi fahimtar yanayin gudanar da aiki a kasashen da suke fama da matsaloli a kan iyakoki don ganin yadda za a iya samar da cikakkun hanyoyi na warwarewa domin kada su shafi sauran wurare da suke da zaman lafiya.”

Da yake nasa jawabin, sakatare janaral na kungiyar jami’in lura da kan iyakoki ta duniya Dr. Kunio Miku-Riya cewa ya yi, lokaci ya wuce da aikin jami’an Kwastum zai takaita kawai kan tara kudin shiga, dole ne su rinka lura da tsaron kan iyakoki, domin muddin babu tsaro a kan iyakoki zai yi wahala gwamnati ta samu kudin shigar da take bukata.

“Abin damuwa sau daya ’yan ta’adda suna yawan kai hari ga jami’an kwastam wanda wannan al’amari ne da ya kamata a hada karfi da sauran hukumomin tsaro wajen musayar bayanan sirri tare da kara samar da na’urorin aiki na zamani don inganta tsaron kan iyakoki.”

Daga karshen ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa karbar bakuncin wannan babban taro da ta yi wanda aka assasa shi shekaru 37 da suka gabata.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)